A yayin taron manema labaru da aka yi, ministan tattalin arzikin kasar Mexico Bruno Ferrari ya bayyana cewa, a yayin taron, ministocin tattalin arziki da ciniki na kasashe mambobin kungiyar G20 sun yi musayar ra'ayoyi, tare da cimma daidaito kan kin yarda da samar da kariyar ciniki, sun kuma sha alwashin kauce wa tsara sabbin matakan kayyade ciniki. Ya kara da cewa, ra'ayi daya da aka samu a yayin taron shi ne samar da kariyar ciniki zai sanya masu saye-saye su kara kashe kudi yayin da za a kara biya 'yan kwadago albashi da yawa. Sa'an nan kuma, hakikanin halin da ake ciki ya nuna cewa, yin ciniki ba tare da kafa shinge ba yana iya raya tattalin arziki kai tsaye.
Kafin wannan kuma, Chen Deming, ministan kasuwancin kasar Sin ya jaddada cewa, tilas ne a yi hattara da kariyar ciniki, a ci gaba da kin yarda da samar da kariya a harkokin ciniki. (Tasallah)