Wasikar ta ce, kungiyar EU za ta sanar da kokarin da ta yi wajen tinkarar rikicin bashi ga kungiyar G20, kana za ta bayyana wa kasashe masu halartar taron, niyyarta wajen tabbatar da cikakken yanki mai amfani da kudin Euro da kuma tsarin kudi. An jaddada a cikin wasikar cewa, ana fatan kasar Girka za ta cika alkawarinta da kuma ci gaba da zama a cikin kungiayar mai amfani da kudin Euro. Haka zalika , za a sa kaimi ga samun ci gaban tattalin arziki bisa tsari bai daya a yankin yayin da ake kiyaye yin amfani da kudi iri daya a yankin.
A cikin wasikar, Van Rompuy da Barroso, sun yi kira ga manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya, da su bada taimako wajen daidaita tattalin arzikin duniya, kana sun yi imani da cewa, shirin sa kaimi ga samun babban ci gaba na kungiyar G20 na birnin Los Cabos da za a zartas a gun taron koli na kungiyar G20 a wannan karo, zai bada taimako wajen tabbatar da tsarin kudi, da kyautata shi yadda ya kamata.
Wasikar ta jaddada cewa, za a maida hankali kan yadda za a kara samar da aikin yi, musamman ma ga matasa. A gun taron, an yi maraba da kungiyar G20 domin tana ci gaba da yi lura kan batun samar da aikin yi.
Ban da wannan kuma, kakakin babban sakataren MDD Eduardo Del Buey, ya bayyana a wannan rana cewa, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya riga ya mika wata wasika zuwa ga taron koli na kungiyar G20 da za a gudanar a kasar Mexico.A cikin wasikar ya yi kira ga kasashen duniya da su warware rikicin rashin aikin yi ta hanyoyin zuba jari, manufofi ,da kuma matakan sa kaimi ga samar da aikin yi.(Zainab)