A cikin rahoton, Mr Li ya bayyana cewa, samun bunkasuwa ya dogara da yin kwaskwarima, abin da ya kasance wani muhimmin mataki saboda ganin ci gaban da aka samu cikin shekaru 36 da suka gabata, da kuma nasarar da aka samu wajen tinkarar mawuyacin hali a shekarar bara.
Don hakan inji shi ya kamata a dogara a kan matakin yin kwaskwarima domin neman samun bunkasuwa nan gaba. Ya lura da cewa ya zuwa yanzu, ana fuskantar mawuyacin hali wajen gudanar da kwaskwarima, saboda haka, ya kamata, a sauke nauyin dake wuyan shugabanni da lasan takobin aiwatar da kwaskwarima tare da daukan matakai da suka dace.
Firaministan na Kasar Sin Mr Li ya nuna cewa, yin kwaskwarima ya kasance wani shiri mai inganci kuma abin da zai samar da amfani, shi ya sa ya kamata, a sa jama'a sun ci gajiyar kwaskwarima da ake yi, wanda ya kasance matakin da za a dauka nan gaba wanda ba za a iya canjawa ba. Ya bada shawarar cewa, ya kamata a kafa wani tsari mai amfani cikin adalci, da samun bunkasuwa yadda ya kamata, ta yadda jama'a za su samu moriya.(Amina)