Li ya bayyana cewa, a shekarar da ta wuce, an sami babban ci gaba wajen bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Amurka Barack Obama sau biyu inda aka samu nasara sosai. Sa'an nan jimillar kudin cinikayya tsakanin kasashen biyu ta kai sama da dala biliyan 500. A matsayin Sin da Amurka na kasa mai tasowa mafi yawan jama'a, da kasa mai sukuni mafi girma a duniya, yin mu'amala da hadin gwiwa tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare zai sa kaimi ga yunkurin kafa sabuwar dangantaka tsakaninsu, da tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa da walwala a shiyya-shiyya da duniya baki daya.
A nasa bangare, mista Kerry ya ce, yin shawarwari masu ma'ana da hadin gwiwa tsakanin Amurka da Sin na da muhimmanci kwarai da gaske.(Fatima)