Gabanin ranar bikin bazanar na gargajiyar kasar Sin, firaministan kasar Li Keqiang ya kai ziyara a lardin Shaanxi dake yammacin kasar Sin a ranar jiya Lahadi, domin ganawa da wasu mutanen dake fama da talauci, musammun ma tsoffin da ba su da muhallin zama da kananan yara marayu, inda ya yi alkawarin yin iyakacin kokarinsa domin tabbatar da mawadaciyar zaman rayuwa ga wadannan mutane, ta yadda kowa zai samu gida. Ya kara da cewa, bikin bazana na gargajiyar kasar Sin yana muhimmancin gaske ga Sinawa, wadanda suke dora babban muhimmanci kan zaman iyali da iyaye. Ya kamata, mu yi iyakacin kokarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a, ba ma kawai mu kula da zaman rayuwarsu na da kullum ba, har ma mu kwantar da hankalinsu, kuma yin haka wata babbar kauna ce dake bayyana halayyar Sinawa ta asali, in ji mista Li Keqiang. (Amina)