in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta amince ta tsagaita wuta
2013-12-28 16:44:34 cri
Mahukunta a kasar Sudan ta Kudu sun bayyana aniyar su, ta kawo karshen dauki ba dadi da dakarun ta ke yi da 'yan adawa. Koda yake gwamnatin ta ce za a iya kaiwa ga cimma wannan buri ne kadai, idan har 'yan tawaye suka dakatar da kai mata hare hare. Wakilan gwamnatin kasar ne suka bayyana hakan yayin wani taron jagororin Gabashin Afirka da ya gudana a kasar Kenya.

Koda yake babu wani wakili daga tsagin 'yan adawar kasar da ya halarci taron. Duk da haka dai mahukuntan kasar Sudan ta Kudun sun bayyana cewa basu da niyar kwatar birnin Bentiu, hedkwatar jihar Unity mai arzikin man fetir daga hannun 'yan adawar. Wannan dai alkawari na zuwa ne bayan da tuni dakarun gwamnatin kasar mai ci suka kwato jihar Upper Nile wadda a baya ke karkashin ikon 'yan adawar.

Jihar Unity dai yanzu haka na hannun dakaru masu biyayya ga korarren mataimakin shugaban kasa Riek Machar, mutumin da mahukuntan Sudan ta Kudun suka zarga da shirya juyin mulkin sojin da bai yi nasara ba. Tuni dai Machar ya musanta hannu cikin waccan balahira, yana mai cewa dauki ba dadin da ya auku rikici ne tsakanin dakarun kasar masu banbancin ra'ayi.

Don gane da batun hawa teburin shawara kuwa, Machar ya ce gwamnatin kasar mai ci bata martaba sharuddan aiwatar da shawarwarin ba, ciki hadda bukatar sakin magoya bayan tsagin 'yan adawar kasar. Ya ce sakin 'yan siyasar nan 9, da mahukuntan kasar ke tsare da su yanzu haka na cikin muhimmin matakin fara tattaunawa.

Rahotannin baya bayan nan dai na nuna cewa, tashe-tashen hankula dake aukuwa a Sudan ta Kudu sun raba akalla mutane 121,600 da gidajen su, adadin da ofishin tsare-tsare, na hukumar bada agajin jin kai ta MDD OCHA yace na iya zartawa, duba da cewa adadin bai hada da al'ummun dake wurare masu karancin jama'a ba.

A wani batun mai alaka da wannan kuma, helkwatar MDD ta tabbatar da isar jami'an 'yan sanda 72 birnin Juba helkwatar Sudan ta Kudu, a ranar Juma'a 27 ga watan nan. Jami'an 'yan kasar Bangladash, a baya na gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya ne a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo. Suna kuma cikin rukunin farko, na karin dakarun wanzar da zaman lafiya 5,500, da kwamitin tsaron MDD ya amince a tura kasar Sudan ta Kudun.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China