Kakakin fadar ta White House Caitlin Hayden ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Talata, inda ta ce, sassan biyu za su aike da wakilai zuwa Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, don yin tattaunawa bisa shiga tsakanin kungiyar raya gwamnaticin gabashin Afirka.
Jami'ar ta yi kira ga shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar, da su hanzarta daukar matakan da suka dace, don kawo karshen rikicin.
Ta ce, kasar Amurka ta damu matuka da halin da ake ciki a Sudan ta Kudu, ganin yadda fararen hula ke ci gaba tagayyara. Don haka, Amurkan ke ci gaba da kira da tsaigata bude wuta, ta yadda za a daidaita lamarin don a samar da kayayyakin agaji ga fararen hulan da ke matukar bukatar taimako. (Ibrahim)