in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin tsagaita wuta a Sudan ta Kudu na tattare da kalubale
2013-12-28 21:12:25 cri
Kawo yanzu kudurin gwamnatin Sudan ta Kudu na tsagaita wuta tsakanin ta da tsagin 'yan adawa na fuskantar tarin kalubale, sakamakon rarrabuwar kawuna da bangarorin Biyu ke fama da shi.

Ba da jimawa ba ne dai mahukuntan Sudan ta Kudun suka ayyana burin su na dakatar da kaiwa yankunan da 'yan adawa ke rike da su hare-hare, suna masu bukatar 'yan adawar su amince da hawa teburin shawara. Sai dai kawo yanzu abu ne mawuyaci a iya tabbatar da ko wannan mataki zai yi tasiri ko kuwa a'a.

Da yake maida martan kan wannan batu, tsohon mataimakin shugaban kasar, da shugaba Salva Kiir ya kora, Riek Machar, wanda kuma ke jagorantar tsagin masu adawa da gwamnatin mai ci, yace kawo yanzu gwamnatin kasar bata dauki matakan gudanar shawarwari ba. Daga nan sai ya jaddada bukatar sakin magoya bayan sa da gwamnatin ke tsare da su, matakin da a cewar sa na da muhimmancin gaske ga shirin sulhu da ake fatan gudanarwa.

Wannan dai hali na kiki-kaka da bangarorin biyu suka shiga, ya kawo babban cikas, ga burin kasashen duniya na ganin an warware rikicin siyasar kasar cikin lumana.

Tuni dai wata hukuma mai rajin samar da ci gaba ko IGAD a takaice, ta yi kashedin cewa, za ta dauki tsattsauran mataki kan duk bangaren da ya yiwa shirin ta na warware rikicin kasar ta Sudan ta Kudu kafar ungulu. Matakin da ake ganin na iya janyo hankalin bangarorin Biyu su rungumi hanyar sulhuntawa.

Don gane da hakan Abdul-Hamid Awad, mai fashin baki kan harkokin siyasa na kasar Sudan, kuma babban editan jaridar Alqarar ta birnin Khartum, na ganin matsin lambar da kasashe masu ruwa da tsaki da ma ragowar kasashen duniya ke yi, ya sanya shugaba Kiir amsa kiran da aka yi na daukar matakan sulhu, ciki hadda sakin mutanen da gwamnatin sa ke tsare da su.

A wani batu mai alaka da wannan kuma, kakakin rundunar sojin Sudan ta Kudu Philip Aguer ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Sin Xinhua cewa, basu samu wani umarni na dakatar da bude wuta ba, don haka ne ma a cewarsa kawo yanzu suke ci gaba da yunkurin dakile ayyukan 'yan tawayen kasar.

Duk dai da muhimmiyar rawar da ake ganin IGAD na iya takawa a wannan batu, a hannu guda masu nazarin yanayin siyasar Sudan ta Kudun na ganin kokarin hukumar na iya fuskantar kalubale, sakamakon kyakkyawar alakar IGAD din da gwamnatin kasar mai ci. (Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China