Kakakin Sojin kasar Philip Aguer ya sheda ma kamfanin dillancin labarai ta Xinhua ta wayar tarho daga Juba babban birnin kasar Sudan ta kudu cewa lallai ana cigaba da gwabzawa tsakanin bangarorin biyu amma ba zai iya bada cikakken bayani a kan yanayin da ake ciki ba.
Yayi bayanin cewa ya zuwa wannan lokacin suna jiran sakamako ne daga filin daga game da halin da ake ciki sakamakon fadan da ya barke lokacin da sojojin magoya bayan Machar suka kai hari ga sansanin sojan dake Malakal da niyyar karbe ikon shi.
A wani labarin kuma ance sojojin magoya bayan Machar sun karbe ikon mallakar garin na Malakal wanda anan ne aka fi samun albarkatun mai a kasar.
Kamar yadda jaridar dake da ofishi a kasar Faransa,Sudan Tribune ta bada rahoto ta yanar gizonta ance mazauna garin na Malakal da dama sun tabbatar da cewa mummunan fada ya auku a safiyar ranar talata kuma zuwa yammacin wannan rana sojoji masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar sun karbe ikon wannan gari. (Fatimah Jibril)