Yau Litinin 15 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta yi bayani game da ziyarar da shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al-Bashir ya kai a kasar Sudan ta kudu, inda ta ce Sin ta gamsu tare da yabawa ga hakan domin ya kasance muhimmin ci gaba da kasashen biyu suka samu wajen kyautata dangantakar dake tsakaninsu. Don haka in ji ta kasar Sin na fatan kasashen biyu za su yi amfani da zarafi mai kyau domin ci gaba da daidaita wasu matsaloli a tsakanin su.
An ba da labari cewa, Shugaba Omar Hassan Al-Bashir ya kai ziyara a kasar Sudan ta kudu a ran 12 ga wata, abin da ya nuna cewa, kasashen biyu sun yi mu'ammala yadda ya kamata, inda shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit shi ma ya ce, yanzu kasashen biyu na cimma matsaya daya kan batun fitar da man fetur da cinikayyar shige da fice a iyakokin kasashen biyu. (Amina)