in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta yi kokari wajen kyautata dangantakar dake tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu
2013-10-23 17:08:03 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a gun taron manema labaru a yau Laraba 23 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Sin ta yi maraba da ziyarar da shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya kai a Sudan ta Kudu a kwanakin baya da kuma yadda shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito kan batutuwa da dama.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a ranar Talata 22 ga wata, shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir da takwaransa na kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit sun yi shawarwari da gabatar da wata sanarwa a birnin Juba, inda suka cimma daidaito kan batun gaggauta gina yankin iyakar kasa da ba na soja ba da batun Abyei da dai sauransu.

Game da wannan, Hua ta bayyana cewa, kasar Sin tana fatan kasashen Sudan da Sudan ta Kudu za su ci gaba da warware matsalolinsu ta hanyar yin shawarwari cikin lumana bisa ka'idar fahimtar juna. Kana Sin za ta ci gaba da yin kokari tare da kasa da kasa wajen kyautata da inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China