A lokacin ganawar sa da manema labarai Kakakin majalissar Martins Nesirky yace ofishin ya yi maraba da sabuwar majalisar zartarwas da aka nada a gwamnatin kasar da a yau ita ce karama a duniya.
A ranar laraba ne dai Shuagaban kasar Salva Kiir Mayardit ya nada sabuwar majalisar zartarwas gwamnatinsa sakamakon rushe na baya da ya yi talatan data gabata.
Ofishin Majalisar a kasar ta Sudan ta kudu,inji Mr Nesirky, za ta yi aiki da wannan majalisar zarwarwas da zaran an rantsar da su domin share fagen fuskantar kwaskwarima da ake shirin yi da suka hada da yaki da cin hanci da rashawa,bangaren tsaro da kuma samar da ababen more rayuwa ga al'umma.
Kakakin majalisar har ila yau ya tabbatar da shirin ofishin na ganin ta yi aiki tare da gwamnatin yadda ya kamata wajen kare lafiyar fararen hula, inganta manyan cibiyoyin kasar da ayyukan duba kwaskwarima da za'a yi ma kundin tsarin mulkin kasar sannan da ganin an aiwatar da babban zabe cikin lumana da kwanciyar hankali.
Ofishin majalisar na UNMISS dai an bude shi ne a shekara ta 2011,kuma yana ayyuka ne kawai ta wajen taimakawa inganta tsaro da kuma ganin an samar da nagartaccen yanayi na cigaba.(Fatimah Jibril)