in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sudan ta kudu ya salami mataimakinsa
2013-07-24 09:56:46 cri
Labarai dake fitowa daga Juba na mai nuna cewa, a ranar Talatan nan shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir ya salami mataimakinsa, Riek Machar, ya rusa majalisar zartaswa kana ya dakatar da babban mai yarjejeniya da kasar Sudan, bisa dokar ikon shugaban kasa.

Mai Magana da yawun Machar ya tabbatar da sallamar Machar daga mukaminsa kamar yadda gidan talbijin na kasar ya ba da rahoto, yayin da jaridar Tribune ta Sudan ita ma ta bada rahoton cewa, an dakatar da aiki da Pagan Amun, babban mai yarjejeniya da Sudan yake yi, dangane da wasu batutuwa da ba'a warware su ba, kuma za a yi bincike a kansa. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China