A cikin wata sanarwa da ofishinta ya fitar, jami'ar ta ce ta kadu matuka da tabarbarewar yanayin jin kai a yankin Pibor na jihar Jonglei,inda aka katse fararen hula kusan 100,000 daga samun tallafin jin kai saboda fadace-fadace.
Sanarwar ta ce fada tsakanin dakarun gwamnatin da wadanda bana gwamnati ba,fadan kabilanci na baya-bayan nan,suna barazana ga rayuwar jama'a kana sun gurgunta kokarin kungiyoyin jin kai na samar da taimakon gaggawa.
Don haka, Madam Amos ta yi kira ga dukkan bangarori da su daina fada nan take,don rage karuwar hasarar rayuka,tare da samar da yanayin tsaron da ya dace don samar da tallafin jin kai.
Bugu da kari ta bayyana cewa,MDD za ta yi aiki da dukkan bangarori don tabbatar da cewa,an samar da taimakon jin kai ga mutanen da ke bukata. Ta kuma tunatar da dukkan bangaroin, da su mutunta dokokin jin kai na kasa da kasa game da kare fararen hula.
Jonglei dai ita ce jiha mafi girma a gabashin Sudan ta kudu,kuma tana fuskantar fadan kabilanci tun lokacin da Sudan ta kudu ta samu 'yan cin kanta a ranar 11 ga watan Yulin shekarar 2011 daga Sudan karkashin yarjejeniyar lumana. (Ibrahim)