in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mbeki ya bukaci Khartoum ta kara hakuri don a samu warware matsala da Sudan ta kudu
2013-07-26 09:57:38 cri
Shugaban tawagar aiwatarwa ta kungiyar hadin kan kasashen Afirka dangane da batun Sudan (AUHIP) Thabo Mbeki, a ranar Alhamis ya bukaci kasar Sudan da ta bada karin lokacin yin kokarin warware matsaloli dake tsakaninta da kasar Sudan ta kudu.

Mbeki ya isa birnin Khartoum tare da rakiyar ministan harkokin waje na kasar Habasha Tedros Adhanom, inda ya tattauna da shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir.

Ya ci gaba da bayyanawa 'yan jarida cewa, an kafa kwamitoci biyu, daya na dauke da nauyin duba yankin da aka hana fadace-fadace, kana na biyu zai duba korafi da Sudan ta gabatar na cewa Sudan ta kudu na bada goyon baya ga 'yan tawaye, inda ya ci gaba da cewa a yanzu haka wadannan kwamitoci an kafa su kuma sun fara aiki, don haka ya dace a basu lokaci domin su gabatar da ayyukansu.

Kwamitocin biyu zasu gana da shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit don kasashen biyu su duba yadda zasu shawo kan wadannan batutuwa su kuma ci gaba da yin hadin gwiwa.

Mbeki ya tabbatar da cewa kwamitin da aka dorawa nauyin duba yankin da aka hana fadace-fadace zai isa kan iyakokin nan da kwanaki biyu, kana daya kwamtin mai duba batun goyon bayan 'yan tawaye ya riga ya fara aiki. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China