Rahotanni daga Tashkent, babban birnin kasar Uzbekistan, na cewa an cimma daidaito, kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi bunkasa tattalin arzikin duniya da na shiyya shiyya, da kuma batun hadin kai a fannonin tattalin arziki, da cinikayya da raya al'adu, a tsakanin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO.
Taron wanda shi ne karo na 12 da aka gudanar a ranar 29 ga wata ya samu halartar wakilai da dama, an kuma yi musayar ra'ayoyi tare da cimma matsaya daya. Bugu da kari kasashe mambobin kungiyar ta SCO, sun daddale yarjejeniyoyi masu muhimmanci da dama, tare da fidda hadaddiyar sanarwar bayan taron. (Danladi)