in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron firayin ministocin kasashe mambobin kungiyar SCO karo na 12
2013-11-29 20:43:46 cri

An bude taron firayin ministocin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO karo na 12 a yammacin ranar Jumma'a 29 ga wata a Tashkent, babban birnin kasar Uzbekistan, inda firayin ministocin da suka zo daga kasashe mambobin kungiyar, da wakilai daga kasashe masu sa ido guda 5, da manyan jami'ai daga MDD da {ungiyar tarayyar kasashe masu 'yancin kai da dai sauran kungiyoyin duniya sun halarci taron budewa.

Ana kyautata zaton cewa, za a daddale yarjejeniyar saukin jigilar kaya a hanyoyin kasa a tsakanin kasashe mambobin kungiyar SCOa gun taron, a kokarin kara daga matsayin mu'ammalarsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya da al'adu, da kuma ciyar da tattalin arzikinsu gaba. Ban da wannan kuma, firayin ministocin da ke halartar taron za su tattauna kan yadda mambobin kungiyar suka hada kansu a fannoni daban daban a shekarar da ta gabata, da nazari kan halin da suke ciki a halin yanzu, da aiwatar da ra'ayi daya da suka samu a gun taron koli na Bishkek, da rarraba ayyukan da za a gudanar da su don yin hada gwiwa a tsakanin mambobin. Bayan taron kuma, za a bayar da wani bayanin bayan taro.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China