Jakadar kungiyar kawancen kasashen Turai dake kasar Tunisiya Laura Baeza ta bayyana a ran 28 ga wata cewa, EU ta mai da hankali sosai kan rikicin siyasa da ya auku a kasar Tunisiya.
A wannan rana kuwa, jakadun 17 na kasashen Turai dake Tunisiya sun yi shawarwari da wakilan manyan kungiyoyi hudu a kasar. Baeza ta yi kira ga jam'iyyun kasar ta Tunisiya da su kai ga matsaya daya na yin hakuri da juna, ta yadda za a tabbatar da mika mulkin kasar. Ban da haka, a cewarta, tana fatan kasar ta Tunisiya ta zartas da sabon tsarin mulki tun da wuri tare kuma da gudanar da zabe a fili cikin adalci, da kuma kafa wata gwamnati mai wa'adin shekaru 4 ko 5 mai dorewa, hakan zai warware matsalar tattalin arziki da al'umma da kasar ke fuskanta yanzu.
An ba da labari cewa, tun bayan da an kai hari kan mambar majalisar adawa da gwamnati Mohamed Brahmi a ran 25 ga watan Yuli, rikicin siyasa ya rutsa da dukkan kasa. Ko da yake, babbar kungiyar siyasa ta kasar ta kira wani taro a ran 5 ga watan Oktoba tare kuma da daddale taswirar magance rikici, amma bangarori daban-daban ba su cimma matsaya daya kan wanda zai kama mukamin firaministan gwamnatin wucin gadi, hakan ana fuskanta halin kila-wa-kila har ila yau. (Amina)