in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunisiya za ta dauki matakan yaki da yin sumogar kayan abinci
2011-07-28 11:06:39 cri
Ranar Laraba 27 ga wata, hukumomin cinikayya da yawon shakatawa na kasar Tunisiya sun ba da sanarwar cewar, gwamnatin wucin gadi ta kasar za ta dauki matakai masu tsanani domin yaki da yin sumogar da ajiye kayan abinci ta yadda za a tabbatar da biyan bukatun mutane a lokacin watan azumi.

Sanarwa ta ce, muhimman kayayyakin da kasuwannin kasar sukan samar kamar su sukari, garin shinkafa, man ja, shayi da sauransu sun sami gatanci daga gwamnati domin biyan bukatun jama'a. Saboda haka, duk wanda ya yi sumoga da ajiye irin wadannan kayayyakin, za a yanke masa hukunci. Sanarwa ta nemi hukumomin da abin ya shafa da su kara karfin sa ido domin tabbatar da biya bukatun jama'a.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China