Kamar yadda gidan talabijin din kasar ta sanar, firaministan ya jaddada cewa gwamnatin sa ba za ta cigaba da makalewa a karagar mulki ba, amma dai za ta sauke nauyin dake kan wuyan ta.
Wannan sanarwar ta Ali Larayedh ta zo kwanaki 4 bayan kissan gillar da aka yi ma Mohammed Brahmi, babban mai hamayya da gwamnatin Ennahdha a majalissar mulkin kasar.
Tun bayan wannan kissan gillar, daruruwan mutane suka bazama a kan tituna suna kiran da gwamnati ta sauka daga mulki. (Fatimah)