Kakakin ma'aikatar harkokoin wajen Amurka Victoria Nuland ta fada a wani taron manema labarai cewa, "Tashin hankali ba zai samu gindin zama a tsarin demokuradiyar kasar Tunisia ba, sannan ba zai warware batutuwan da Tunisia ke fuskanta ba kuma kissan gillar ba shi ne mafita ba, domin ba abin da zai haifar illa tashin hankali."
Nuland ta bukaci 'yan kasar ta Tunisia da su bayyana abin da ke damunsu cikin lumana, kana daga bisani ta yi kira ga jami'an tsaro da su rika nuna hakuri.
Kalaman na Nuland sun zo ne bayan da aka harbe Chokri Belaid, shugaban jam'iyyar adawa ta Popular Front har lahira a ranar Laraba da safe a wajen gidansa da ke Tunisia.
Sakamakon wannan kisan gilla, firaministan Tunisia Hamadi Jebali a ranar Laraba ya bayyana shirinsa na kafa sabuwar gwamnatin kwarraru da ba na 'yan siyasa ba domin su jagoranci kasar kafin a gudanar da zabe.(Ibrahim)