A ranar litinin 'yan ta'adda sun kashe sojojin Tunisiya guda 8 a kusa da tsaunukan Chaambi, dake dab da kan iyakar kasar da kasar Aljeriya, inda hakan ya kara tsananta rikicin siyasa.
Kamfanin dillancin labaran kasar APS ya bada rahoto cewa Ould Kabila ya bayyana cewa dakarun sojin kasar (ANP) sun kara karfinsu da kuma kayan aiki ta gabashin kan iyakar kasar, dangane da yanayin rashin cikakken tsaro a Tunisiya.
Ould Kabila ya bayyana hakan ne yayin da Firaminsitan Aljeriya Abdelmalek Sellal ke ziyarar yankin Tiaret, mai tazarar kilomita 350, kudu maso yammacin babban birnin kasar, Algiers.
Ould Kabila ya bada tabbacin cewa akwai musayar bayanan tsaro tsakanin kasar Aljeriya da kasashe makwabtanta domin a yi yaki da miyagu dake kawo barazana ga tsaro da dorewar yankin, da suka hada da ta'addanci da dukkan wasu ayyuka na shigowa da kayayyaki ba bisa doka ba. (Lami Ali Mohammed)