Kulab din kasar ta Tunusia dai na da shirin buga karin wasannin 3, na share fagen shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka dake tafe nan da 'yan kwanaki, wasannin da aka shirya bugawa a hadaddiyar daular Larabawa ta UAE, wadanda kuma kulaf din ke fatan kammalawa kafin ranar 22 ga watan nan, wato ranar da zata buga wasan farko na cin kofin nahiyar Afirka da kasar Algeria a birnin Rustenburg na Afirka ta kudu.