in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Tunisiya ya yi kira da a kara saurin bunkasa kungiyar UMA tare
2012-11-25 16:32:10 cri
A ranar Asabar 24 ga wata a birnin Tunis, shugaban kasar Tunisiya, Moncef Marzouki ya yi kira da a kara saurin bunkasa kungiyar tarayyar kasashen dake yankin Maghreb (UMA), a kokarin cimma burin bunkasa wadannan kasashe da jama'arsu dake wannan yanki tare.

A wannan rana, lokacin da yake jawabi a wajen bikin bude taron shawarwarin koli na kungiyar UMA, Moncef Marzouki ya ce, ana da tarihi daya, al'ada daya, kuma ana bin addini daya a yankin Maghreb, amma aikin neman samun bunkasuwa bai daya yana kasa da kashi 2 cikin dari bisa dukkan ayyuka a wannan yanki, idan aka kwatanta da sama da kashi 80 cikin dari da kasashe membobin kungiyar EU suke da shi a nasu.

A don haka, in ji shi, kamata ya yi kasashe membobin kungiyar UMA su kara azama wajen samun bunkasuwa tare da juna, a kokarin cimma burin jama'arsu na samun ci gaba tare.

Haka kuma Shugaba Moncef Marzouki ya bayyana cewa, kasar Tunisiya na fatan ci gaba da kokarin sa kaimi ga wannan batu, da karfafa yin shawarwari da bangarori daban daban da abin ya shafa, da kuma zurfafa dangantakar abokantaka tsakaninta da sauran kasashe makwabta, musamman ma kasar Libya, a kokarin cimma burin kammala aikin kafa kungiyar UMA cikin shekaru 10 masu zuwa, ta yadda za a samar da makoma mai kyau ga jama'ar dake wannan yanki.

Shugabannin kasashen Algeria, Morocco, Mauritania, Libya, Tunisiya da sauran kasashen yankin sun halarci wannan taron shawarwarin kolin a kan bunkasa kungiyar UMA da neman samun ci gaba tare a birnin Tunis.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China