Ran 6 ga watan Fabrairu, Hamadi Jebali ya sanar da cewa, zai kafa wata karamar gwamnatin kwararru cikin mako guda bayan kisan gillar da aka yi wa wani jagoran adawa, kana idan ya kasa, zai yi murabus.
Ya sanar da kasawar tasa ran 18 ga wata, sabo da manyan jam'iyyu biyu a kasar da suka hada da jam'iyya mai sassaucin ra'ayin Islama da jam'iyyar al'ummar kasa sun yi watsi da shirinsa.
Yayin ganawa da manena labarai, Hamadi Jebali ya bayyana cewa, ya bayar da sanarwar murabus din tasa ga gwamnati mai ci don cika alkawarinsa, amma dukkan ma'aikatan gwamnatin za su ci gaba da ayyukansu har zuwa kafuwar sabuwar gwamnati a kasar. (Maryam)