A ranar 6 ga wata ne, aka harbi Belaid da harsasai 4 a kansa da kirjinsa yayin da yake hanyar zuwa aiki, inda daga karshe, ya mutu a asibiti, firaministan kasar Tunisiya kuma shugaban jam'iyyar Ennahdah Hamadi Jebali ya yi Allah wadai da wannan kisan gilla mai alaka da siyasa, amma ya bayyana cewa, ba a tabbatar da su wane ne maharan ba, a sa'i daya kuma, jam'iyyar Ennahdah ta musunta da gudanar da wannan lamari.
Shugaban kasar Tunisiya Moncef Marzouki da ke ziyara a kasashen Turai ya yi Allah wadai da wannan lamari, kuma ya soke tafiyarsa ta ranar Alhamis zuwa Masar don halartar taron koli na kungiyar hadin gwiwar kasashen da ke bin addinin Musulunci da za a yi.
Bayan da aka samu labarin mutuwar Belaid, masu zanga-zanga kimanin 8000 sun yi zanga-zanga a wajen ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar, inda suka bukaci gwamnati mai ci yanzu ta sauka daga mulki, kuma masu zanga-zanga sun yi arangama da 'yan sanda..(Bako)