Sa'ilin da yake jawabi a wani taron manema labarai tun bayan fara zaben, Kameel Jendoubi shugaban hukumar zabe ta kasar (ISIE) ya ce, da wuya a iya bayyana adadin wadanda suka fita don kada kuri'unsu a wannan lokaci
An fara kada kuri'un ne da karfe 7 na safe agogon kasar, daidai da karfe 6 na safe agogon GMT, kana an ci gaba da yin hakan har zuwa karfe 7 na maraice a agogon Tunisiyar, karfe 6 a agogon GMT, zaben da ake fatan fitar da mambobin majalisar su 217, da zasu yi aikin tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar da za'a yi amfani da shi wajen gudanar da zabukan majalisar dokoki da na shugaban kasa cikin watanni 12.
Kafar yada labarai ta kasar Tunisiya (TAP) ta ambato Beji Caid Essebsi, firaministan rikon kwarya na kasar, bayan kada tasa kuri'ar a mazabar Ariana dake arewacin babban birnin kasar a ranar Lahadin yana cewa, ba ja da baya a harkar gudanar da zaben. Kana ya nuna gamsuwa game da yadda kasar ta zage wajen bunkasa 'yancin cin gashin kai da ci gabanta.
Kimanin 'yan kasar miliyan bakwai da dubu dari uku da suka cancanci kada kuri'a ne zasu zabi wakilansu daga cikin jam'yyun siyasa 77, da wasu na gamayya guda biyu, da daruruwan 'yan takara marasa jam'iyyu. Baki daya dai kimanin 'yan takara dubu 11 ne suke gogayyar samun kujera a majalisar tsarin mulkin.
Litinin din nan ake sa ran sanar da sakamakon karshe na zaben, wanda yayin gudanar da shi aka jibge jami'an tsaro 40,000, kama daga kan 'yan sanda zuwa sojoji.
A tarihin zaben kasar, karon farko an bar masu sanya ido kan zabe daga kasashen waje su bibiyi kadin zabukan, wadanda kuma manema labarai na kasashen waje su 600 za su ba da rahotanni a kai. (Garba)