Firaministan Libya Ali Zaidan ya shaidawa taron manema labarai bayan ganawar cewa, manufar ganawar, ita ce tattauna batun hanyoyin inganta matakan tsaro a kan iyakokin kasashen, yaki da shigar bakin haure ba tare da izni ba da kuma simogan miyagun kwayoyi da makamai.
Zaidan ya jaddada cewa, kasashen uku, sun amince su rika ganawa sau 3 a shekara, bisa la'akari da tasirin da rikicin kasar Mali ya haifar.
Harkokin tsaro sun tabarbare a kasashen guda uku ne, tun bayan rikicin da ya barke a kasar Libya a shekara ta 2011, lamarin da ya sa ake ta simogan makamai, sace mutane da hare-haren makamai a kan iyakokin kasashen.
Sai dai bayan ganawar ministocin ta ranar Asabar, an ji karar harbin bindiga a kusa da wurin da aka yi taron, kuma har yanzu ba a san dalilin yin wannan harbi ba kuma ba wani rahoto game da wanda ya jikkata. (Ibrahim)