in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An amince da jerin sunayen sabbin ministocin gwamnatin kasar Tunisiya
2013-03-14 14:59:37 cri

A ran 13 ga wata nan, cikakken taron majalisar dokokin kasar Tunisiya, ya zartas da takardar jerin sunayen sabbin ministocin gwamnatin kasar, da firaministan kasar Ali Laarayedh ya mika masa.

Sabuwar gwamnatin kasar dai na kunshe da ministoci 27, da sakataren harkokin kasar 10, an kuma kara walilai uku a matsayin minista wadanda ke kula da siyasa, da tattalin arziki, da mulkin yaki da cin hanci da karbar rashawa, wadanda kuma kai tsaye karkashin jagorancin firaministan kasar.

Daga cikin wadannan ministoci, akwai mutane masu zaman kasu guda 4, da za su zama ministoci, ciki hadda ministan harkokin cikin gida, da na harkokin waje, da na tsaron kasa da kuma na shari'a, yayin da wasu masana a fannoni daban-daban, suka samu matsayin ministan ilmi, da na na'urori, da na sadarwa da sauransu. Sai kuma ministocin da za su ci gaba a kan mukamansu, ciki hadda na sha'anin gona, da na kiwon lafiya, da na sufuri, da kuma ministan kula da harkkin Bil Adam da sauransu (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China