in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sassa daban daban sun nuna ra'ayoyinsu kan babban taron Durban
2011-11-26 17:03:44 cri
MDD za ta shirya babban taro kan sauyin yanayi a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu a ran 28 ga wata. A jajibirin budewar taron, sassa daban daban masu ruwa da tsaki sun bayyana ra'ayoyinsu kan taron.

Madam Christiana Figueres, sakatariyar zartaswa ta ofishin sakatariya mai kula da 'yarjejeniyar tsarin MDD kan sauyin yanayi' ta jaddada cewa, ana bukatar samun ci gaba a fannoni 2 a yayin taron Durban, wato aiwatar da ajandar ayyuka da aka tsara a yayin taron Cancun na Mexico a bara da kuma sa kaimi kan tsara wani wa'adi na daban na ci gaba da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli bisa takardar Kyoto.

Kwamitin kungiyar Tarayyar Turai wato EU ya ba da wata sanarwa, inda ya yi fatan cewa, ya kamata a tabbatar da shirin taswira kan ayyukan rage fitar da iska mai dumama yanayi bayan shekara ta 2012, in ba haka ba, EU ba za ta amince da tsara wani wa'adi na daban ba kan ci gaba da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli.

Todd Stern, manzon musamman na kasar Amurka kan sauyin yanayi ya ce, kasarsa ba za ta tattauna da saura kan takardar Kyoto a taron Durban ba. Sa'an nan John Ashton, wakilin musamman na ma'aikatar harkokin wajen kasar Birtaniya kan sauyin yanayi ya furta cewa, kasarsa na fatan sauran kasashe masu sukuni za su yi alkawarin kara rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China