in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mulatu Teshome ya zama sabon shugaban kasar Habasha
2013-10-08 15:51:28 cri

Tarrayar majalisar dokokin kasar Habasha ya sanar a ran 7 ga wata cewa, Mulatu Teshome wanda jam'iyyar dake rike da mulkin kasar ta gabatar da shi ya zama sabon shugaban kasar, wanda kuma ya maye gurbin Girma Wolde Giorgis da ya dade yana wannan mukami har tsawon shekaru 12.

Mulatu Teshome jakadan kasar Habasha dake kasar Turkiya dan shekaru 57 a duniya, ya taba zama jakadan kasar dake kasashen Japan, Australiya, Sin da dai sauransu, ban da haka, ya taba zama ministan raya tattalin arziki da hadin kai na kasar, ministan sha'anin noma da shugaban majalisar dokokin kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China