Firaministan kasar Habasha kuma mai rike da shugabancin karba-karba a kungiyar AU Hailemariam Dessalegn ya nuna a ran 14 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Sin da Afirka na da dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, wadda ke bin ka'idar adalci, mutunta juna da kuma kawo moriyar juna.
Hailemariam Dessalegn ya bayyana hakan ne yayin jawabi mai jigon "Zumunci dake tsakanin Sin da Afrika da bunkasuwa da kwaskwarima a karkashin sabuwar dangantakar hadin gwiwa" a jami'ar koyon harsunan kasashen ketare ta birnin Beijing.
Bugu da kari, Hailemariam Dessalegn ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, Sinawa dake gudanar da aiki a nahiyar Afrika sun kawo manyan sauye-sauye ga nahiyar, inda manyan ababen more rayuwa da suka yi a Afrika sun gaggauta tsarin dunkulewar Afrika.
Saboda hakan yake maraba da kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a wasu karin fannoni, ciki hadda sha'anin samar da kayayyaki, harkar noma da dai sauransu. (Amina)