Wani jami'in ma'aikatar watsa labaru ta kasar Habasha ya furta a ran 15 ga wanan wata cewa, sojojin gwamnatin kasar Habasha sun kai farmaki ga dakarun kasar Eritrea a wannan rana.
Ministan gudanarwa na ma'aikatar watsa labaru ta kasar Habasha Shimelis Kemal ya bayyana a gun taron manema labaru da aka yi a yammacin wannan rana da cewa, sojojin gwamnatin kasar sun tsallaka iyakar kasa daga yankin arewa maso gabashin kasar zuwa kasar Eritrea a ranar 15 ga wannan wata da safe. Daga baya sun dakile dakaru a yankuna biyu na kasar Eritrea dake da nisan kilomita 16 zuwa iyakar kasa.
A shekarar 1993, kasar Eritrea ta samu yancin kai ta fita daga cikin kasar Habasha. A watan Mayu na shekarar 1998, kasashen Habasha da Eritrea sun yi musayar wuta mai tsanani a sakamakon neman mallakar yankunan dake iyakarsu. Duk da cewar, kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar shimfida tabarmar zaman lafiya a tsakaninsu a shekarar 2000, amma sun ci gaba da samun sabani da yawa a kan batun iyakar kasa. Gwamnatin kasar Habasha ta zargi gwamnatin kasar Eritrea da horar da dakarun dake iyakar kasa domin nuna adawa da gwamnatin kasar Habasha.(Lami)