Wannan kyautar za'a gabatar da ita a karon farko a ranar 26 ga watan Maris na shekarar 2012 a Addis Abeba, babban birnin kasar Habasha a gabanin bude zaman taron ministocin kudi na kasashen Afrika da za'a bude a birnin a kalla cikin wannan wata, in ji kungiyar CEA a ranar Talata a cikin wata sanarwa.
A cewar wannan sanarwa, taron zai maida hankali kan ayyukan da suka wajaba domin mayar da Afrika a matsayin wani sabon dandalin bunkasuwa domin cigaban tattalin arzikin duniya. Kuma kyautar ta shekara shekara nada manufar zurfafa ilimi a fannin kimiyya, fasaha da baiwa ga matasa maza da matan Afrika musamman ma bunkasa hanyoyin kirkirowa tare da babbar dama ga harkokin kasuwanci. (Maman Ada)