An yi jana' izar marigayi Meles Zenawi a cocin Holy Trinity dake a Addis Abeba, hedkwatar kasar Habasha bayan an gudanar da wani bikin nuna juyayi a dandalin Meskel a gaban idon shugabannin kasashen Afrika da dama, wakilan gwamnatocin sauran nahiyoyin duniya inda a cikinsu akwai mataimakin faraministan kasar Sin Hui Liangyu, da kuma 'yan kasar Habasha kimanin dubu 60.
A lokacin da yake jawabi albarkacin bikin jana'izar, mataimakin faraminista kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya nuna cewa Meles ya kasance babban jarumi wanda ya kai kasarsa bisa sabuwar makoma, kuma wanda yayi gwagwarmayar neman cigaban al'ummar kasarsa har ma da ta nahiyar Afirka.
Shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan, da yake jawabi a yayin bikin jana'izar ya bayyana cewa har kullum sai an tuna da taimakon da Meles ya ba da ga cigaba da zaman lafiya a kasarsa da ma nahiyar Afrika.
Hakazalika shugaban Najeriya ya yabawa taimakon da Meles ya kawo Afrika a matsayin kakakin nahiyar game da matsalar sauyin yanayi da kuma matsayinsa na shugaban kwamitin tsara manufofi na shugabanni da gwamnatoci kan sabon tsarin dangantakar cigaban Afrika na Nepad. (Maman Ada)