Meles Zenawa dai ya rasu a cikin daren ranar Litinin zuwa ranar Talata a wani asibitin kasar waje. Tuni gwamnatin kasar ta shiga cikin zaman makoki, haka kuma an sauko da tutocin kasar kasa. Bisa ga yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, mataimakin faraministan kasa yake zama faraministan kasa na wucin gadi. (Maman Ada)