Yau Talata 21 ga wata, gidan telibijin na kasar Habasha ya ba da labari cewa, firaministan kasar Meles Zenawi ya rasu a daren ran 20 ga wata sakamakon ciwo, mataimakinsa kuma ministan harkokin waje na kasar Hailemariam Desalegn zai zama mukaddashin firaministan kasar.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a cikin watanni biyu da suka gabata, Meles Zenawi wanda ke da shekaru 57 a duniya ya yi jiyya a kasashen waje. Amma a daren ran 20 ga wata, rashin lafiyar ta kara tsananta, abin da ya yi sanadiyar mutuwarsa da karfe 11 da mintoci 40 na dare. Sai dai ba a bayyana ko wace cuta ce ya kamu da ita ba, kuma ba a bayyana wurin da ya yi jiyyar ba.
An ba da labari cewa, a watan Yuli na wannan shekara, Meles Zenawi bai halarci taron koli na kungiyar tarayyar Afrika AU ba da aka yi a birnin Addis Ababa, abin da ya jawo hankali mutane sosai.
An haifi marigayi Meles Zenawi ne a gundumar Adwa dake arewacin kasar Habasha, wanda ya zama shugaban kasar daga shekarar 1991 zuwa ta 1995, kuma daga shekarar 1995 zuwa yanzu ya rike mukamin firaministan kasar.(Amina)