Gidan talabijin na kasar Habasha ya ba da rahoto a ranar Talata cewa, marigayi Zenawi mai shekaru 57 da haihuwa, ya mutu ne a ranar Litinin da dare, sakamakon wata cutar da ya kamu da ita yayin da ya ke murmurewa a asibitin da ya ke jiyya a kasashen waje.
A cikin wata sanarwar da kakakin Ban Ki-moon Martin Nesirky ya bayar, ya ce, "za a tuna da firaminista Zenawi saboda kyakkyawan shugabancinsa, dukufa kan batutuwan da suka shafi Afirka a ciki da wajen nahiyar, da kuma mayar da hankali wajen bunkasa tattalin arzikin kasar."
Sanarwar ta ce, babban sakataren na MDD ya ji dadin yadda gwamnatin Firaminista Zenawi ta kasance mai goyon bayan kokarin shirin wanzar da zaman lafiya na MDD. baya ga shigar dakarun kasar Habasha cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya da dama a Afirka, ciki har da Sudan, Liberia da kuma Burundi.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, Mr Ban har ila yau, ya godewa marigayi Zenawi bisa ga himmatuwarsa na yin aiki da MDD a ayyukan wanzar da zaman lafiya da dama a duniya da kuma kalubale daban-daban, da muhimmiyar rawar da ya taka a shirin sassantawa da ke gudana tsakanin Sudan da Sudan ta kudu, manufofin muradun karni da matsalar canjin yanayi.
Sanarwar ta ce, "A wannan lokacin da ake makokin mutuwar firaministan, babban sakataren na MDD ya sake nanata kudurin MDD na yin aiki kafada da kafada da gwamnati da kuma al'ummar kasar Habasha".
Marigayi Zenawi ya kasance shugaban gwamnatin wucin gadi na kasar Habasha daga shekara 1991 zuwa 1995 lokacin da aka zabe shi a matsayin firaministan kasar kana ya kasance a wannan matsayi har zuwa wannan lokaci.(Ibrahim)