A cikin wata sanarwar da aka fitar daga fadar shugaban kasar Najeriya, shugaba Jonathan ya bayyana mutuwar Zenawi a matsayin wani babban rashi ga nahiyar Afrika.
A cewarsa, Zenawi babban shugaban kasa ne na Afrika, abokin kasar Najeriya dake kuma bautawa al'ummar kasar Habasha.
Haka kuma za'a ci gaba da tunawa da tsinkaye da imanin Zenawi kan kafa wata al'ummar adalci da cigaba, in ji shugaban Najeriya.
Hakazalika ya yabawa tunanin Zenawi na ganin Afrika mai karfi da hadin kai. (Maman Ada)