Kuma shugaban kasar na Najeriya zai koma kasarsa a wannan rana ta lahadi bayan ya halarci wannan jana'izar, a cewar wata sanarwa ta fadar shugaban kasar.
Mista Meles Zenawi ya rasu a wani gidan asibitin birnin Bruxelles na kasar Belgique a ranar 20 ga watan Augusta kuma za'a jana'izarsa a wannan rana ta lahadi a Addis-Abeba.
Shugaban Goodluck Jonathan ya bayyana bacin rai da juyayi sosai bayan ya samu labarin mutuwar Meles Zenawi.
Hakazalika mista Jonathan ya nuna cewa mutuwar Zenawi wani babban rashi ne ga nahiyar Afrika, kuma ya bayyana Zenawi a matsayin babban shugaba a Afrika, kuma abokin kasar Najeriya, wanda ya gina kasarsa tare da bautawa jama'ar Habasha. (Maman Ada)