Haka kuma ministan watsa labaru na kasar Habasha Bereket Simon ya bayyana a yayin wani taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, cewar an zabi Demeke Mekonnen, ministan ilmi na kasar da ya zama mataimakin shugaban jam'iyyar a yayin taron jam'iyyar na kwanaki biyu.
Mr. Bereket ya kara da cewa, sabon shugaban Jam'iyyar EPRDF da kuma mataimakinsa za su fara aikinsu a matsayin firaministan kasar Habasha da mataimakinsa, kuma bayan da aka samu amincewa daga majalisar dokokin kasar, Mr. Hailemariam da Mr. Demeke za su yi rantsuwar kama aiki a farkon watan Oktoba na bana.
Tsohon firaministan kasar Habasha Meles Zenawi mai shekaru 57 da haihuwa, ya riga mu gidan gaskiya a ranar 21 ga wata Agusta a birnin Brussels, babban birnin kasar Belgium, wanda ya tsaya kan karagar mulkin kasar har na tsawon shekaru 21. Bayan rasuwarsa, nan da nan an nada mataimakinsa Mr. Hailemariam a matsayin mukadashin firaminista kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.(Kande Gao)