Ya zuwa yanzu, babu wata kungiya da ta sanar alhakin kai wadannan hare-hare. Manazarta suna tsammani cewa, bisa wuraren da aka kai hare-hare da hanyar da aka kai harin, watakila kungiyar masu tsattsauran ra'ayi kamar kungiyar al-Qaeda ce ta kai hare-haren.
An samu kyautatuwar halin da ake ciki a kasar Iraki idan aka kwatanta shi da wasu shekaru da suka gabata, amma a kan samun rikice-rikice a wasu lokuta a kasar. A ranar 16 ga wata, an kai hare-hare fiye da 10 a birnin Kerkuk dake arewacin kasar Iraki, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwa da raunatar mutane a kalla 60. (Zainab)