An kai harin kunar bakin wake a ran 23 ga wata a birnin Tuz Khurmatu dake arewacin Iraqi, inda lamarin ya yi sanadiyar asarar rayukan mutane tare da jikkata fiye da dari.
'Yan sandan sojin Iraqi sun bayyana cewa, yayin da ake bikin jana'izar iyalin wani jami'in darikar Shi'a a wani masallacin dake wurin, sai wani mutum da ya yi damara da bom a jikinsa ya kutsa kai cikin masallacin ya kuma ta da bom din.
Ya zuwa yanzu, an tabbatar da mutuwar mutane 42, yayin da wasu 75 suka samu rauni ciki hadda shugaban jihar Salahuddin. Rudunar tsaron kasar sun riga sun rufe wannan yanki.
Saboda irin mummunan rauni da wasu mutane suka samu ana ganin cewar mai yiwuwa ne adadin wadanda suka mutu zai karu.
Babu wani ko wata kungiya da suka sanar da daukar alhakin aiwatar da lamarin. Wani manazarci ya nuna cewa, kila mambobin darikar Sunni su ne suka kai harin. (Amina)