A wannan rana, an kai hare-haren boma-bomai guda 2 a Kirkuk da ke da nisan kilomita 300 arewa da birnin Baghdad hedkwatar kasar Iraq, inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 21, tare da jikkatar wasu sama da 200. A kuma wannan rana, an kai hare-haren boma-bomai guda 3 a birnin Baghdad hedkwatar kasar, wanda shi ma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5. haka kuma, an kai harin kunar bakin wake a birnin Fallujah da ke yamma da birnin Baghdad, kuma harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6 ciki har da wani dan majalisar dokoki.
A wannan rana, shugaban majalisar dokokin kasar Usama al-Nujayfi da ministan kudi na kasar Rafie issawi wadanda ake ganin an kai don a hallaka, sun tsallake rijiya da baya cikin harin bom da aka kai a birnin Samarra da ke arewa da yammacin birnin Baghdad. Wannan shi ne karo na 2 da aka yi yunkurin kashe wannan ministan kudi dan Sunni na kasar cikin mako guda.(Bako)