Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare-haren, amma a yawancin lokuta kungiyar al-Qaida da ke kasar ta Iraki ce ke kai irin wadannan munanan hare-hare a kasar.
Kasar Iraki dai tana fuskantar tashin hankali mai tsanani cikin shekaru biyar, abin dake haifar da fargaba cewa, zubar da jini na baya-bayan yana kokarin sake jefa kasar shiga yakin basasa irin wanda ya barke a shekarar 2006 da shekarar 2007, inda yawan mutanen da ke mutuwa a kowane wata a wasu lokutan ya kan zarta 3,000. (Ibrahim Yaya)