Wani dan sanda da ba ya son a fadi sunansa ya bayyana cewa, a wannan rana da dare, a yankin Sadr City dake arewa maso gabashin birnin Bagadaza, inda 'yan darikar Shia suke da sansani, an samu fashewar boma-bomai sau biyu da aka dasa cikin mota, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 10, yayin da wasu 32 suka jikkata.
Ya kara da cewa, a wannan rana da dare kuma, an samu fashewar boma-bomai a yankin Jihad dake kudu maso yammacin birnin. Yayin da wata motar 'yan sanda take kan hanyar yin sintiri, aka kai mata harin boma-bomai ita ma har sau biyu da aka dasa a gefen hanya. Hakan ya haddasa mutuwar wani dan sanda, yayin da wasu mutane 6 suka ji rauni, ciki har da 'yan sanda guda 2.
Baya da haka, a kusa da birnin Baqouba, cibiyar jihar Diyala dake gabashin kasar Iraki, an samu fashewar boma-bomai da aka dasa cikin wata mota da kuma harin harbi sau daya, wadanda suka haddasa mutuwa da kuma jikkatar mutane da yawa.
Dadin dadawa, kafin wannan kuma, a wannan rana, an samu jerin fashewar boma-bomai a wurare daban daban na kasar Iraki da nufin kai hari kan Musulmai 'yan darikar Shia da sojojin kiyaye tsaro. Mutane sama da 20 ne suka mutu, yayin da wasu fiye da 10 suka jikkata a sakamakon haka.(Fatima)