An kai harin da ya fi hallakar mutane ne a birnin Hilla inda aka fi samun Musulmai 'yan shi'a suke zaune, da ke kudu da nisan kilomita kimanin 100 zuwa birnin Bagadaza, kuma hare-haren boma guda biyu da aka dasa cikin mota an kai su ne kan Musulmai 'yan shi'a da ma'aiktan tsaro da suka je ceton mutane, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 26 tare da jikkatar wasu 80, a sa'i daya kuma, hare-haren biyu daban da aka kai a waje da birnin Bagadaza sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Ban da kuma, a ranar 29 ga wata, an kai harin bom da aka dasa cikin mota a birnin Kerbala, inda Musulmai 'yan shi'a da ke yankin kudancin kasar suke zaune, kuma abin da ya hallaka da raunana jama'a fiye da 10, haka kuma, an kai hare-hare ga sojoji da 'yan sanda a birnin Fallujah da ke yammacin kasar, da birnin Mosul da ke yankin arewacin kasar.
Manazarta sun bayyana cewa, kungiyar ta'addanci da dakarun da ke adawa da gwamnatin kasar suka sake kai hare-haren ta'addanci a wurin, domin lahanta kokarin gwamnatin Iraqi da ma'aikatan tsaro wajen samar da zaman lafiya a kasar.(Bako)