A ran 3 ga wata 'yan sandan kasar Iraqi sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun kai hari kan hedkwatar 'yan sanda dake lardain Kirkuk a arewacin kasar Iraqi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 30 yayin da wasu 70 suka jikkata.
Wani dan sandan Iraqi ya bayyana cewa, da sanyin safiyar ranar Lahadi 3 ga wata ne 'yan bindigar su biyu suka kutsa da wata mota da ake makare da boma-bomai cikin ginin hedkwatar 'yan sandan, sannan suka tashi ababan fashewar inda nan take motoci da dama suka kama wuta, a karshe kuma 'yan sanda sun tarwatsa su
Daga baya, an gano wasu karin 'yan bindiga a kalla 33, dake sanye da tufar 'yan sanda, wadanda ke cikin maharan.
Ya zuwa yanzu, babu wani daidaikun mutane, ko wata kungiyar da ta sanar da daukar alhakin kai wannan hari, sai dai wani mai binciken yadda lamarin ke wakana ya ce, kila hare-haren da aka kai kwanan baya, na da alaka da ayyukan kungiyar Al-Quaeda, wadda ke da zummar rura wutar rikici tsakanin darikar Shi'a da Sunni, da kuma rage karfin gwamnatin Nuri Al-Maliki dake goyon bayan darikar Shi'a. (Amina)