Yayin da wani jami'in 'yan sanda na lardin Babil da ba ya son a bayyana sunansa ke zantawa da wakilinmu, ya ce, an kai harin bam ne a wani titin da ke cibiyar birnin Musayyib da ke lardin, lokacin da wasu Musulmi 'yan shi'a suka dawo daga birnin Karbala, suna tsaye a bakin titin inda harin ya ritsa da su. A cikin mutanen da suka mutu ko jikkata, har da wasu mata da yara. Sabo da ganin wasu mutane sun samu rauni mai tsanani, yawan mutanen da suka rasu zai iya samun karuwa.
Yanzu, haka dai, babu wata kungiya ko mutum da ya dauki alhakin kai harin.(Bako)