Cikin laifukan da ake tuhumar Mubarak da sauran mabiyansa, akwai laifin ba da umarni ga yin amfani da makamai don tarwatsa masu zanga-zanga, kana da sayar da iskar gas ga Isra'ila bisa farashi mai rahusa, tare da laifin cin hanci da rashawa. Ana dai sa ran gudanar da wannan shari'a ne a babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta 10 dake birnin Al'kahira na kasar ta Masar.
A halin yanzu, Mubarak mai shekaru 84 na samun kulawar likitoci a wani asibitin soji na kasar. Idan dai za a iya tunawa a farkon shekarar 2011 ne, aka yi zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar ta Masar, lamarin da ya janyo hambarar da Mubarak daga mukaminsa. Bisa kididdigar da kafofin yada labaru suka yi, an ce, mutane kimanin 850 ne suka rasu cikin rikicin.(Bako)